13 Yuli 2021 - 11:58
​Nijar: Sojoji 4 Sun Rasa Rayukansu Yayin Da ‘Yan Ta’adda 40 Suka Halaka

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da mutuwar dakarun kasar 4 da fararen hula 5, yayin da kuma ‘yan bindiga akalla 40 suka halaka a jiya, sakamakon gurmurzun da aka yi tsakanin bangarorin biyu a yankin yammacin kasar.

ABNA24 : Rahoton da gidan rediyon Faransa ya bayar ya ce, a cikin sanarwar da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar ta ce, ‘yan bindiga masu tarin yawa sun kai hari da misalin karfe 3 na ranar Lahadi a wani gari da ake kira Tchoma Bangou, lamarin da ya sa jami’antsaro suka kai dauki.

Bayanin ya ce, a lokacin wannan hari ne ‘yan bindigar suka kashe fararen hula 5 da kuma sojoji 4, yayin da su kuma a nasu bangaren sojojin suka halaka akalla 40 daga cikin ‘yan ta’addan.

Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa, sojojin sun samu nasarar gano wani wuri da ‘yan ta’addan suke boye Babura da suke yin amfani da su wajen kai hare-hare, da kuma tarin makamai da suka hada da manyan bindigogi.

Garin da aka yi gumurzun dai yana kusa da iyaka da kasar Mali ne daga yammacin jamhuriyar Nijar, inda a kan yi gumurzu da ‘yan ta’adda a wannan gari lokaci zuwa lokaci.

342/